Ni da babana banda abin fade sai godiya
Dan kamin komai a rayuwar duniya
Sai dai naima addu'a Rabbu yama rahama
Kamar yanda ka raine ni tun ina a zanin goyo
Ana ana bi hibbak
Ya abatiy yiyi
Ya babana...
Ni da baba na nake naka yin tutiya
Zama na dansa na halal, shi ne kwalliya
Ta rayuwa ta, tata a cikin duniya
Antalsababu fi annani wulidtu walidiy
Ya Abati yiyi
Ya babana
Allah ya baka aljanna zama na cikin cikinta kaji dadi har kai mana oyoyooo
Ni ne dan autan baba na shalele
Ni ne dai na gaban goshi, mai Jan kyalle
Kuma ni ne dan albarka, mai kamar atilele
Anta sababu abtisamati walidiy
Ya abati yiyi
Ya gata na ah
Allah yasa na gaji halinka na hakuri, na zamma abun koyo
Mu fada mu gaya musu babanmu yafi na kowa
Sai muyi yar rawa, ban ruwa, karda iyayen mu muyi sabawa
Ni da Baba na
Gata na nana
Mai tausai na
Ya abatiy
Qurrata ayni na
Rabbu yama rahama, kamar yanda ka raineni tun ina a zanin goyo...
Ni da babana
Ni da babana
Ni da babana nake yin tutiya
Ni da Babana banda abun fade sai godiya